Gwamnatocin Ethiopia da Eritrea sun yarda zasu sako dukkan fursunonin yakin juna daga yakin bakin iyakarsu da ya kare shekaru biyu da suka shige.
A yau Jumma'a Ethiopia ta ce zata sako fursunonin Eritrea su dubu 1 da 300, kwanaki kadan a bayan da Eritrea ita ma ta yarda ta sako dukkan fursunonin Ethiopia su 300.
Wannan sanarwa ta zo a bayan da shugaban kungiyar agaji ta Red Cross na duniya, Jakob Kellenberger, ya ziyarci dukkan kasashen biyu.
Mr. Kellenberger ya gana da shugabannin dukkan kasashen biyu lokacin wannan ziyarar tasa.