Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Tana Neman Goyon Bayan Kasashen Waje, Yayin Da Amurka Ke Kara Nuna Mata Yatsa - 2002-08-27


A yayin da Amurka take kara nuna yatsa ma kasar Iraqi, hukumomi a birnin Bagadaza sun kaddamar da wani kyamfe a fagen diflomasiyya domin dakuse barazanar farmakin soja.

A birnin Bagadazar, shugaba saddam Hussein ya shaidawa ministan harkokin wajen daular Qatar cewa Iraqi ta cika dukkan sharrudan da aka tilasta mata bi karkashin kudurorin Kwamitin Sulhun MDD. Shugaban na Iraqi ya ce barazanar da Amurka take yi ta kai farmaki kan Iraqi, tana yi ne da dukkan kasashen Larabawa.

Ministan harkokin wajen na Qatar, Sheikh hamad bin Jasim bin Jabir al-Thani, ya ce makasudin wannan ziyara tasa shine ceto yankin daga barazanar farmakin soja. Ya roki Iraqi da ta amince da komawar sufetocin makamai na MDD.

A halin da ake ciki, mataimakin shugaban Iraqi, Taha Yasin Ramadan, ya fara rangadin kasashen Sham (Syria) da Lebanon, a wani bangaren yunkuri a fagen diflomasiyya. Kafin ya bar Bagadaza, Malam Ramadan ya shaidawa wata jaridar Iraqi cewa kyale sufetocin MDD su koma Iraqi ba zai hana Amurka kai farmakin soja ba.

A jiya litinin mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney ya fito da kakkausar harshe yana fadin cewa ya kamata a kai harin "rigakafi" a kan Iraqi. Ya ce babu shakka Saddam Hussein yana da makaman kare-dangi, kuma yana shirin yin amfani da su a kan Amurka da kawayenta.

Ya ce da yawa daga cikin jami'an gwamnatin shugaba Bush sun yi imanin cewa "nan ba da jimawa ba" Iraqi zata mallaki makaman nukiliya. Mr. Cheney ya ce illar rashin daukar mataki ta zarce na daukar matakin nesa ba kusa ba.

XS
SM
MD
LG