Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Zai Karbi Bakuncin Jakadan Sa'udiyya A Gonarsa Ta Texas - 2002-08-27


Shugaba Bush yana karbar bakuncin jakadan Sa'udiyya na nan Amurka a gonar kiwon dabbobinsa dake Jihar Texas, inda zasu tattauna.

An bada rahoton cewa a yau talata shugaba Bush da Yarima Bandar bin Sultan zasu ci abincin dare tare.

Har ila yau Mr. Bush zai dauki yariman na Sa'udiyya domin yin rangadi da shi zuwa wuraren da ya fi kauna cikin wannan gona mai fadin eka 650.

Ana sa ran tattaunawar da zasu yi zata maida hankali kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa, da yaki da ta'addanci wanda a cewar kakakin fadar White House, Ari Fleischer, yana iya hadawa da Iraqi.

Sa'udiyya tana adawa da daukar kowane irin matakin soja a kan Iraqi, sannan tanada bambancin ra'ayi da gwamnatin shugaba Bush a kan batun rikicin Gabas ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG