Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mura Ta Kashe Mutane 671 A Kasar Madagascar - 2002-08-27


Jami'an kiwon lafiya sun ce yawan mutanen da suka mutu a sanadin annobar zazzabin mura mai tsanani da ake fama da ita a Madagascar, ta karu zuwa 671.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce yawan mutanen da suka kamu da cutar yayi kusan ninkuwa zuwa dubu 20 a cikin makonni biyun da suka shige. Ta ce ana fama da wannan annoba a larduna biyar daga cikin shida na kasar.

Hukumar ta ce daya daga cikin dalilan da suka sa wannan annoba tayi muni sosai a Madagascar shine rashin ayyukan kiwon lafiya a kasar. Har ila yau, hukumar ta ce wannan kywayar cuta dake yada murar mai suna "Type A Influenza", sabuwa ce a kasar ta Madagascar, saboda haka jikin al'ummar kasar bai samu kariyarta ba.

XS
SM
MD
LG