Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilai A Zauren Taron Kolin Alkinta Muhalli Na Duniya Suna Takalar Batutuwa - 2002-08-29


Wakilan dake halartar taron kolin kasashen duniya a kan muhalli a birnin Johannesburg dake Afirka ta Kudu, zasu maida hankali kan yadda za a iya kulla kawance tsakanin gwamnati da sassa masu zaman kansu, a tattaunawar da suke yi yau alhamis.

A yau alhamis Amurka ta gabatar da shawarwari da dama da nufin rage yunwa, da rage iska mai guba dake fitowa daga kona mai, tare da samar da makamashi ga wasu kasashen Afirka.

A jiya laraba, an samu ci gaba a fannin ciniki da bada agaji ga kasashe masu tasowa da kuma kare ruwayen tekun duniya. Amma har yanzu ana dambarwa kan batun rangwamen farashin kayan amfanin gona. Kasashe masu tasowa sun yi kukar cewa rangwamen da kasashe masu arziki suke yi wa farashin amfanin gonarsu, ya sa amfanin gona daga kasashe masu tasowa ba ya iya yin takara a kasuwannin duniya da na kasashen masu arziki.

Babban burin wannan taron koli na kwana goma, shine kawar da talauci tare da bunkasa tattalin arzikin kasashe ba tare da lalata albarkatun kasa ba. Shugabannin kasashe 100 ake sa ran zasu halarci wannan taron koli kama daga ranar litinin.

XS
SM
MD
LG