Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kara Yanke Hukumce-Hukumcen Kisa Ta Hanyar Jefewa A Nijeriya - 2002-08-29


Wata kotun Shari'ar Musulunci a Nijeriya ta yanke hukumcin kisa ta hanyar jefewa kan wani mutumi tare da wata macen da aka samu da laifin yin zina.

Jami'ai a Jihar Neja, sun ce an yanke hukumcin na kisa a kan Ahmadu Ibrahim da Fatima Usman, duka masu shekaru talatin da wani abu, bayan da suka amsa cewa sun tara a lokacin da ita Fatima Usman take da aure. Fatima ta yi ciki ta kuma haihu a sanadin wannan dangantaka tasu.

A karkashin dokokin Shari'ar Musulunci, ana yanke hukumcin kisa kan mai aure ko wanda ya taba yin aure, aka kuma same shi da laifin yin zina.

Tun da fari a yau alhamis, wata kungiyar kare hakkin Bil Adama tayi tur da wani hukumcin na kisa da aka yanke kan Ado Baranda cikin makon nan a Jihar Jigawa. A cikin watan Mayu aka samu Ado Baranda da laifin yin fyade ma wata yarinya karama 'yar shekaru 9 kacal da haihuwa.

Kungiyar "Human Rights Watch" ta ce ba a yi shari'ar gaskiya ma shi Ado Baranda ba. Shi dai Ado, mai shekaru hamsin da wani abu da haihuwa, an ce ya amsa wannan laifi nasa, kuma ya ki yarda ya daukaka kara.

XS
SM
MD
LG