Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Ce Tilas Majalisar Dinkin Duniya Ce Kawai Zata Iya Yanke Shawara Kan Iraqi - 2002-08-29


Shugaba Jacques Chirac ya ja kunnen Amurka da ta guji daukar matakin soja na kanta game da kasar Iraqi.

Ya ce Kwamitin Sulhun MDD ne kawai ya kamata ya yanke shawara a kan matakin da za a dauka idan har Iraqi ta ki yarda ta kyale sufetocin makamai su koma kasar ba tare da sharadi ba.

Gwamnatin shugaba Bush ta ce har yanzu Iraqi tana kera makaman kare dangi, kuma barazanar da take yi tana karuwa. A makon nan mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney ya bayyana dalilan da suka sa tilas a kai ma Iraqi harin rigakafi.

Waziri Gerhard Schroeder na Jamus ya ce ya kamata Amurka ta kara tuntubar kawaye tukuna. Sweden ta roki Amurka da ta nemi sanya hannun kasashen duniya wajen warware wannan batu, kada kuma ta dauki wani matakin da zai gurgunta MDD.

Shugaba Chirac na Faransa ya ce idan har Iraqi ta ki yarda sufetocin makamai su koma kasar ba tare da saharadi ba, to MDD ce kawai zata iya yanke shawarar matakan da za a dauka.

Yau kusan shekaru hudu ke nan rabon sufetocin makamai da kasar ta Iraqi.

XS
SM
MD
LG