Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Kasar Sweden Sun Gano Yunkurin Da Suka Ce Na Yin Fashin Jirgin Sama Ne - 2002-08-30


'Yan sanadan kasar Sweden sun kama wani mutumin da suka yana shirin yin fashin jirgin sama dauke da wata bindigar da ya boye cikin jakar da yake dauke da ita.

Hukumomi suka ce an kama wannan mutumi dan kasar ta Sweden, amma dan asalin Tunisiya, jiya alhamis, a lokacin da yayi kokarin shiga cikin jirgin sama a garin Vasteras dake arewa maso yamma da birnin Stockholm. An gano bindigar cikin wata 'yar karamar jakar ajiye sabulu da mai a lokacin bincike.

'Yan sandan na sweden ba su bayyana sunan mutumin ba, ba su kuma bayyana irin bindigar da yake dauke da ita, ko kuma idan akwai harsashi a ciki ba.

Sun dai ce mutumin yana tare da kungiyar wasu mutane su 20 dake kan hanyar zuwa wani taron Musulmi a birnin Birmingham a kasar Ingila. An yi tambayoyi ma sauran mutanen dake cikin wannan kungiya na sa'o'i sannan aka kyale su suka tafi.

Daga bisani, jirgin na kamfanin safarar jiragen saman Jamhuriyar Ireland mai suna "Ryanair" ya ci gaba da tafiyarsa zuwa filin jirgin saman Stansted dake wajen birnin London.

XS
SM
MD
LG