Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, ya fito da kakkausar harshe yana yin tur da kasar Britaniya a zauren taron kolin alkinta muhalli na duniya a Johannesburg, ya kuma lashi takobin ci gaba da aiwatar da shirin sake rarraba filaye.
A jawabin da yayi ga shugabannin duniya dake halartar taron kolin, shugaba Mugabe yayi tur da firayim minista Tony Blair na Britaniya, har ma ya ce masa: "ka je ka rike Ingilarka, ka kyale ni in rike Zimbabwe ta."
Mr. Mugabe ya fuskanci suka mai zafi, musamman daga Britaniya, a saboda manufarsa ta sake rarraba filayen noman kasar. A karkashin wannan manufa, ana korar turawa karfi da yaji daga cikin gonakinsu, ana kwacewa a bai wa bakaken fata.
Wannan jawai na Mr. Mugabe ya taho a bayan da shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu ya bude muhawarar kwanaki uku da shugabannin kasashe fiye da 100 zasu yi kan yadda za a takali talauci da alkinta muhalli a fadin duniya.
Shi ma firayim minista Tony Blair yayi jawabi gaban taron kolin, amma kafin Mr. Mugabe yayi nasa. yayi kira ga dukkan kasashen duniya da su rattaba hannu kan yarjejeniyar Kyoto. Ana ganin wannan kira nasa tamkar shagube ne ga Amurka, wadda har yanzu ta ki yarda ta amince da wannan yarjejeniyar da zata takali batun canjin yanayi a duniya.