Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tony Blair Ya Ce Iraqi Tana Yin Barazana Ta Zahiri - 2002-09-03


Firayim ministan Britaniya, Tony Blair, ya ce Iraqi tana yin barazana ta zahiri, wadda tilas kasashen duniya su magance. Wannan furuci nasa ya zo a daidai lokacin da Iraqi ta kara kaimin kai gwauro da mari a fagen diflomasiyya domin neman goyon bayan kasashen duniya game da barazanar farmakin sojan da Amurka take yi mata.

Mr. Blair ya shaidawa 'yan jarida a Britaniya cewa kokarin da Iraqi take ci gaba da yi na kera makaman kare-dangi, ba abin damuwa ga Amurka kawai ne ba. Ya ce Iraqi tana barazana ta musamman, kuma ta zahiri, ga tsaron yankinta da duniya baki daya.

A nan Washington, sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld ya ce a cikin 'yan kwanaki da makonnin da suke tafe, gwamnatin shugaba Bush tana iya gabatar da karin shaidar irin barazanar da Iraqi take yi.

Wannan furuci nasa, tare da na Mr. Blair, sun biyo bayan kalamun da shugabannin duniya suka yi, inda suka nemi da a yi taka tsantsan, suka kuma yi kashedi game da kai hari na radin kai a kan Iraqi.

Mukaddashin firayim ministan Iraqi, Tariq Aziz, ya ce a shirye Iraqi take ta hada kai da MDD wajen samo hanyar warware wannan tankiya. Amma ya ce Iraqi zata tattauna kyale sufetocin makamai cikin kasarta ne kawai tare da wasu batutuwan kamar na kawo karshen takunkumin da aka sanya mata.

XS
SM
MD
LG