Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Rahoton Da Sabiyawan Bosniya Suka Buga Ya Musanta Abkuwar Kisan Gilla A Srebrenica - 2002-09-03


Wani sabon rahoton da gwamnatin 'yan kabilar Sabiyawan Bosniya ta buga, ya yarda cewa an kashe Musulmi dubu biyu a lokacin ad sojojin Sabiyawa suka kwace garin Srebrenica a shekarar 1995.

Sai dai kuma, ta ce akasarinsu sojoji ne da aka kashe a lokacin fada.

Wannan rahoto, wanda shine na farko da hukumomin Sabiyawa suka taba bugawa game da abubuwanda suka wakana a Srebrenica, ya ce Musulmi guda 100 sun mutu a saboda gajiya, wasu guda 100 kuma suka mutu a hannun 'yan kabilar Sabiyawa dake daukar fansa.

Musulmi maza, magidanta da yara, su kimanin dubu 8 suka bace a Srebrenica a bayan da sojojin Sabiyawa suka kwace wannan gari da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a zaman tudun-na-tsira, a yankin gabashin kasar Bosniya.

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka ce Sabiyawa ne suka yi kisan kiyashi ma wadannan mazajen Musulmi.

Babban jami'in shiga tsakani na kasa da kasa a Bosniya, Paddy Ashdown, yayi tur da wannan rahoto da Sabiyawan na Bosniya suka buga.

XS
SM
MD
LG