Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Colin Powell Ya Fuskanci Suka Da Ahir - 2002-09-04


An yi ta kuwwa tare da yin ahir da sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, a lokacin da yake yin jawabi gaban taron kolin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, kan alkinta muhalli da kawar da talauci a Johannesburg, a kasar Afirka ta Kudu.

'Yan kungiyoyin jama'a da na kare muhalli sun yi ta kuwwar nuna Allah wadarai a lokacin da sakatare Powell yake fadin cewa Amurka tana gudanar da wani shirin dala miliyan dubu 1 domin yakar iskar nan mai guba dake kara dumama duniya.

Har ila yau Mr. Powell ya ce Amurka ta rungumi raya kasa ta hanyar tabbatar da kare muhalli, tana kuma shirin kara yawan agajin da take bayarwa na ayyukan raya kasa da kashi 50 daga cikin 100 a shekaru ukun dake tafe.

Sai da jami'an tsaro suka yi awon gaba da 'yan zanga-zanga guda biyu daga cikin zauren wannan taro.

'Yan rajin kare muhalli suna dorawa Amurka laifin dakushe kaifin yarjejeniyoyin da aka riga aka kulla kan kare muhalli.

Da yawa daga cikin kungiyoyin kare muhallin sun fice daga zauren wannan taron a fusace domin nuna rashin jin dadinsu.

A yau laraba aka shirya kammala wannan taron koli na kwanaki goma, inda za a amince da wani shirin da ba dole ne wata kasa ta yi aiki da shi ba, wanda yayi kiran da a kara yawaita amfani da makamashin da za a iya sabunta shi.

XS
SM
MD
LG