Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Tunisiya Sun Sako Madugun Adawa Daga Kurkuku - 2002-09-04


Hukumomin Tunisiya sun ce an sako madugun 'yan adawa, Hamma Hammami, bisa sharadi daga gidan kurkuku a saboda dalilai na rashin koshin lafiya.

An sako shi kwanaki biyu a bayan da kotun kolin Tunisiya ta sake tabbatar da hukumcin daurin watanni 38 da aka yi masa a kurkuku saboda shigarsa cikin jam'iyyar Kwaminis haramtacciya.

A cikin watan fabrairu aka daure Mallam hammami a kurkuku, bayan da ya fito daga buyar da yayi ta shekaru 4 domin ya daukaka karar yanke masa hukumcin da aka yi a shekarar 1999.

Wata lauyar masu rajin dimokuradiyya kuma matar Malam, Hammami, nadia Nsaraoui, ta tabbatar da labarin sako shi yau laraba. Ta ce tana farin cikin iyalanta sun sake haduwa wuri guda. Sai dai kuma ta ce sharadin da aka shimfida na sako shi yana nufin cewa ana iya sake jefa shi a kurkuku a kowane lokaci. Ba ta yi karin bayani kan lafiyarsa ba.

XS
SM
MD
LG