Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Zai Bayyanawa Taron MDD Dalilansa Na Yin Tsama Da Saddam Hussein - 2002-09-04


Shugaba Bush na Amurka ya ce zai bayyana dalilansa na kokarin daukar mataki kan shugaba Saddam Hussein na Iraqi a jawabin da zai yi ranar alhamisar makon gobe a gaban MDD.

A bayan da ya gana da shugabannin majalisar dokoki a fadar White House yau laraba, shugaban ya ce babu wani zabi na yin shiru kan wannan batu, amma kuma ya ce zai nemi iznin majalisar dokoki kafin ya dauki matakan soja a kan Iraqi.

Har ila yau shugaban ya ce zai tattauna batun Iraqi da firayim minista Tony Blair na Ingila ranar asabar a gandun shakatawa na shugaban Amurka dake Camp David, zai kuma tuntubi sauran shugabannin duniya ta wayar tarho a cikin mako mai zuwa.

Shugaban ya ce Saddam Hussein yana barazana sosai, kuma duniya ce, a cewarsa, zata zubar da mutuncinta idan har aka kyale shi ya mallaki makaman kare-dangi.

Sanarwar da Mr. Bush ya bayar ta ziyarar Mr. Blair ta zo kwana guda a bayan da firayim ministan ya ce Britaniya zata wallafa wata kasida kan kokarin da shugaban Iraqi yake yi na mallakar makaman kare-dangi.

A cewar Mr. Blair, shaidar zata nuna cewa har yanzu shugaba Saddam yana kokarin kera makamai masu guba da na yada cututtuka, kuma yana kokarin mallakar makaman nukiliya.

Mr. Blair yayi amfani da irin wannan kasida ta shaida a shekarar da ta shige domin bayyana irin shaidar da ake da ita a kan Osama bin Laden da kungiyarsa ta al-Qa'ida domin shimfida hujjar Britaniya ta goyon bayan matakan sojan da Amurka ta dauka a Afghanistan.

XS
SM
MD
LG