Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yana Son A Bada Iraqi Wa'adi Cikin Gaggawa... - 2002-09-13


Shugaba Bush ya ce yana neman Majalisar Dinkin Duniya ta zartas da sabon kudurin da zai kunshi wa'adin lokacin da za a bai wa Iraqi na kyale sufetocin makamai su koma kasar, ko kuma ta fuskanci abinda ya kira "martani maras makawa."

A lokacin da yake magana a yau Jumma'a, Mr. Bush ya ce Amurka tana son a dauki matakin cikin gaggawa, kuma ya kamata wa'adin lokacin da za a bai wa Iraqi ya zamo na kwanaki da makonni, ba wai na watanni ko shekaru ba.

Shugaba Bush ya ce yana fatan Saddam Hussein zai mika dukkan makamansa na kare-dangi, sai dai kuma ba ya zaton cewa shugaban na Iraqi zai yi haka.

ACT: BUSH: "The reason I am doubtful is, he's had 11 years to meet the demands, and for 11 long years, he has basically told the United Nations..."

VOICE: Dalilin da ya sa nake tababar (ko zai yarda a raba shi da makaman kare-dangin da ya mallaka) shine, yau shekaru 11 ke nan ana kokarin ganin ya cika wannan ka'ida, kuma a duk tsawon wadannan shekaru 11, babu abinda yayi illa kawai nunawa MDD da kuma duniya cewa shi kam ko a jikinsa.

Wannan furuci na shugaba Bush ya zo a daidai lokacin da sakataren harkokin waje Colin Powell yake kokarin neman goyon bayan kasashen duniya ga wani kudurin MDD da zai bukaci Iraqi ta yi aiki nan take da kudurorin binciken makamai na majalisar.

Mr. Powell zai gana a birnin New York da wakilan sauran kasashe hudu masu kujeru na dindindin a Kwamitin Sulhun MDD, watau Britaniya, China, Faransa da Rasha. Har ila yau ana sa ran cewa Mr. Powell zai gana da ministocin harkokin wajen kasashe fiye da hamsin.

A cikin hirarrakin da aka yi da shi yau Jumma'a aka kuma watsa ta gidajen telebijin, Mr. Powell ya ce yana son ya tabbatar da cewa sauran wakilan Kwamitin Sulhun MDD sun fahimci abinda ya kira, kudurin dake tattare da jawabin da shugaba Bush yayi jiya alhamis gaban babban zauren shawarwarin MDD.

XS
SM
MD
LG