Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yana Tattaunawa Da Wasu Shugabannin Afirka - 2002-09-13


Shugaba Bush yana ganawa da wasu shugabanni 10 daga yankin tsakiyar Afirka a birnin New York, a ranar karshe ta ziyarar da ya kai zuwa Babban zauren Shawarwari na MDD.

Kafin su fara wannan ganawa ta su, jami'an fadar White House sun ce tattaunawarsu zata takali shugabanci na kwarai da kuma bukatar dake akwai ta kawo karshen yake-yake da bakar wahala a nahiyar ta Afirka.

Daga baya a yau Jumma'ar, shugaba Bush zai gana da shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu, da shugaba Paul Kagame na Rwanda, da kuma shugaba Joseph Kabila na Kwango-Kinshasa.

Jami'ai suka ce shugaba Bush da wadannan shugabanni uku daga Afirka zasu tattauna kokarin jaddada karfi da tasirin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattabawa hannu kwanakin baya a tsakanin Kwango da Rwanda. Dukkan kasashen biyu suna zargin juna da laifin kreta haddin wannan yarjejeniya.

A bayan wannan ganawar ce shugaba Bush zai taso ya komo nan birnin Washington.

XS
SM
MD
LG