Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami'an Kasashe 80 Zasu Tattauna Shirin Habaka Tattalin Arzikin Afirka - 2002-09-16


A yau Babban Zauren Shawarwarin MDD zai dakatar da muhawararsa ta shekara-shekara a birnin New York, domin tattauna wani shirin da shugabannin Afirka suka tsara da nufin habaka tattalin arzikin nahiyar tare da rage talauci.

Ana sa ran shugabanni 10 daga Afirka zasu hadu da shugabanni da manyan jami'an wasu kasashe 70 domin wannan tattaunawa da za a wuni ana gudanarwa.

Wannan shirin da zasu tattauna a kai mai suna NEPAD, wasu kasashen Afirka 15 ne a karkashin jagorancin Nijeriya da Afirka ta Kudu da Aljeriya da kuma Senegal suka kaddamar shekara guda da ta shige.

Makasudin wannan shirin shine samo jari dubban miliyoyin daloli daga kasashen waje domin farfado da tattalin arzikin kasashen Afirka, tare da yakar talauci da cututtuka.

Domin rama wa kura aniyarta, su kuma gwamnatocin kasashen Afirka zasu kokarta gudanar da mulki na kwarai, da kaucewa zarmiya da barna, tare kuma da kare hakkin bil Adama.

A halin da ake ciki, wani babban jami'in MDD ya ce bala'in karancin abinci mai tsananin gaske yana barazana ga mutane fiye da miliyan 14 a wasu kasashe 6 na yankin kudancin Afirka. Wannan adadi ya zarce kiyasin farko da miliyan guda.

Wakilin MDD na musamman mai kula da bukatun ayyukan jinkai, James Morris, ya ce wannan bala'i yana kara yin tsanani fiye da yadda kowa ya zata. A watan Mayun da ya shige, jami'an MDD sun yi kiyasin cewa mutane miliyan 12 da rabi suke fuskantar yunwa.

Mr. Morris ya ce mutanen da suka fi fuskantar barazanar suna zaune a kasashen Zimbabwe, Zambiya, Malawi, Lesotho, Swaziland da Mozambique.

Hukumar abinci ta duniya ta ce an yi mata alkawarin agajin sulusin kudi fiye da miliyan 500 ne kawai da take bukata domin samar da abincin gaggawa.

XS
SM
MD
LG