Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Ta Yarda Sufetocin Makamai Su Koma - 2002-09-17


Iraqi ta ce shawarar da ta yanke ta kyale sufetocin makaman MDD su koma cikin kasar ba tare da sharadi ba, ta kawar da duk wata hujjar da Amurka take da ita ta kai mata hari.

Mukaddashin firayim minista Tariq Aziz shi yayi wannan furuci yau talata a birnin Bagadaza, sa'o'i kadan a bayan da babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya bada sanarwar cewa Iraqi ta yarda sufetocin makaman su koma.

Mr. Annan ya ce hukumomin Iraqi sun bayyana masa wannan shawara a cikin wata wasikar da ministan harkokin wajen Iraqi, Naji Sabri, ya mika masa jiya litinin da daddare. Mr. Annan ya ce zai mika wasikar ga Kwamitin Sulhun MDD, da babban sufeton makamai Hans Blix, wadanda zasu hadu su san matakin da za a dauka nan gaba.

Wasikar ta ce Iraqi tana son kawar da duk wata tababar cewa har yanzu tana da makaman kare-dangi ta hanyar kyalewa a gudanar da bincike. Har ila yau ta bukaci Kwamitin Sulhun MDD da ya mutunta diyaucin kasar ta Iraqi.

Wani kakakin fadar White house ya bayyana takardar ta Iraqi a zaman wata dabara ta kaucewa mataki mai tsanani daga Kwamitin sulhun MDD. Har ila yau kakakin yayi kiran da zartas ad sabon kuduri mai tasiri da zai takali irin barazanar da shugaban na Iraqi yake yi.

Mukaddashin Firayim ministan Iraqi, Tariq Aziz, ya ce wannan martani na Amurka ya nuna "aniyarta ta zahiri", wadda ya ce ita ce ta mallakar arzikin man yankin.

Sufetocin makamai na MDD sun bar Iraqi tun shekarar 1998, kuma tun daga lokacin ba a kyale su sun koma ba.

XS
SM
MD
LG