Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Jami'in Gwamnatin Burundi Yayi Kiran Da A Binciki Kisan Gilla - 2002-09-17


Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta kasar Burundi, ya ce wasu sojoji sun kashe mutane 183, akasarinsu fararen hula, a cikin ruwan sanyi a farkon watan nan.

Leonidas Ntibayzi, wanda babban dan majalisar dokoki ne, yayi kiran da a binciki wannan kisan gilla da jami'an yankin da abin ya faru suka bayyana masa.

Mr. Ntibayzi ya shaidawa 'yan jarida yau talata cewa mutanen suna kokarin tserewa ne daga fadan da ake gwabzawa a tsakanin 'yan tawayen kabilar Hutu da rundunar sojojin kasar da 'yan kabilar tutsi suka mamaye, ranar 9 ga watan nan a lardin Gitega na tsakiyar kasar.

Ya ce mutanen sun nemi mafaka cikin wasu gidaje, amma sai wadannan sojoji suka fito da su daga ciki, suka sanya su kwanciya a kasa, sannan suka bi suka harbe su baki daya. Bai bayyana ko sojojin da suka aikata wannan danyen aikin na gwamnati ne ko kuma na 'yan tawaye ba.

XS
SM
MD
LG