Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rwanda Ta Fara Janye Sojojinta Daga Kwango-Kinshasa - 2002-09-17


Rwanda ta janye kashin farko daga cikin sojoji akalla dubu 20 da take da su a kasar Kwango-Kinshasa.

Sojoji kimanin 500 sun tashi a jirgin sama daga garin Kindu a Kwango Kinshasa zuwa Kigali, babban birnin Rwanda. Sojojin Rwanda ne suke rike da akasarin yankunan gabashin Kwango.

A wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a watan Yuli, Rwanda ta yarda zata janye sojojinta. Ita kuma gwamnatin Kwango Kinshasa, ta yarda zata kwace makaman tsageran kabilar Hutu na Rwanda dake kai gwauro da mari cikin kasarta, wadanda kuma suke cikin mutanen da suka haddasa kisan gillar mutane har dubu 800 a Rwanda a shekarar 1994.

Gwamnatin Kwango ta ce ta kama 'yan tsageran kabilar hutu kimanin dubu 2, kuma a shirye take ta maida su zuwa Rwanda.

A tsakiyar yakin basasar Kwango Kinshasa dai, kasashen Afirka 6 ne suke da hannu ciki.

XS
SM
MD
LG