Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Zaben Nijeriya Sun Dakatar Da Aikin Yin Rajista A Wasu Yankuna - 2002-09-18


Jami'an zabe a Nijeriya sun dakatar da shirye-shiryen yin rajistar masu jefa kuri'a a wasu yankunan kasar hudu inda a cikin 'yan shekarun nan aka samu tashin hankali na kabilanci da addini.

An bada sanarwar cewar an dakatar da yin rajistar akalla a wasu yankunan jihohin Bauchi, Binuwai, Nassarawa da Filato a arewacin kasar.

An dakatar da wannan aiki a daidai lokacin da jam'iyyun adawa suke kukar cewa ana tabka magudi ka'in da na'in a wannan aiki na rajistar masu jefa kuri'ar. Daga cikin matsalolin da ake bayyanawa har da kokarin yin rajistar wadanda shekarunsu bai kai ba.

A ranar alhamis aka fara wannan gagarumin aiki na yin rajistar masu jefa kuri'a, wanda shine na farko tun lokacin da aka kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999.

Sau biyu ana dakatar da zabubbukan kananan hukumomi cikin wannan shekara, a wani bangare a saboda matsalolin kundin rajistar masu jefa kuri'a.

XS
SM
MD
LG