Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani jami'in Liberiya Ya Nemi MDD Da Ta Dage Takunkumin Da Ta Sanyawa Kasarsa - 2002-09-18


Ministan harkokin wajen Liberiya yayi kira ga MDD da ta dage takunkumin da ta sanyawa kasarsa, a saboda ya ce yanzu kasar ba ta goyon bayan 'yan tawayen makwabciyarsu Saliyo.

Ministan harkokin waje Monie Captan ya ce yanzu ba a yaki a kasar Saliyo, kuma Liberiya ma tana kyautata al'amuranta a fannoni da dama. Ya ce kasarsa tana son yarfar da abubuwan da suka faru a can baya.

MDD ta kafa takunkumin makamai, tare da haramtawa jami'an gwamnatin Liberiya yin tafiya waje da sayen duwatsun lu'ulu'u daga kasar, a bayan da aka tantance cewar gwamnatin shugaba Charles Taylor tana samar da makamai ga 'yan tawayen dake yakar gwamnatin Saliyo, makwabciyarta a arewa.

Gwamnatin Liberiya tayi ikirarin cewa wannan takunkumi yana gurgunta kokarinta na murkushe 'yan tawayen da suka tayar mata da kayar baya. A makon da ya shige shugaba taylor ya dage dokar-ta-baci, a bayan da dakarun gwamnati suka samu nasarori da dama kan 'yan tawaye.

A jiya talata MDD ta kafa wata kungiyar bada shawara da zata taimaka wajen maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Liberiya. Mr. Captan ya bayyana wannan a zaman matakin da ya dace.

XS
SM
MD
LG