Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Da Shugabannin Majalisar Dokoki Sun Yarda Zasu Yi Aiki tare Wajen Zartas Da Kuduri Kan Iraqi - 2002-09-18


Shugaba Bush da manyan shugabannin majalisar dokoki sun yarda zasu yi aiki tare domin zartas da kuduri a kan Iraqi, kafin zabubbukan da za a yi cikin watan Nuwamba a fadin Amurka.

A bayan da ya gana da manyan shugabanni hudu na majalisar dokokin yau a fadar White House, shugaba Bush ya godewa 'yan jam'iyyun Democrat da Republican a saboda kudurin da suka nuna kan wannan batu, yana mai fadin cewa wannan kuduri na majalisar dokoki zai aike da sako ga duniya cewar da gaske Amurka take yi.

Shugaba Bush ya ce nan da 'yan kwanaki kadan zai aikewa da majalisar dokoki daftarin wani kudurin da zai bada iznin yin amfani da karfin soja a kan Iraqi.

A cewar shugaba Bush, shugaba Saddam Hussein na Iraqi ba zai yaudari kowa ba da alkawarinsa na kyale sufetocin makamai su koma kasar.

A can birnin London, firayim minista Tony Blair na Britaniya yayi kira ga duniya da ta ci gaba da matsa lamba wa hukumomin Bagadaza.

XS
SM
MD
LG