Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Rahoto Ya Ce Mutane 915 Aka Kashe A Rikicin Da Aka Yi A Jos A Shekarar Da Ta Shige - 2002-09-18


Wani rahoton da hukumar bincike ta gwamnati ta buga ya ce mutane har 915 aka kashe a lokacin rikicin addinin da aka yi tsakanin Musulmi da Kirista bara a garin Jos a arewacin Nijeriya.

Wannan adadi na yawan wadanda suka mutu, yayi kusan ninka kiyasin da gwamnatin jihar ta yi a bara. Jami'an gwamnati a Jihar ta Filato, inda aka yi wannan tashin hankali, sun ce suna fargabar wannan rahoton yana iya haddasa wani sabon tashin hankalin.

Wannan tashin hankali na garin Jos ya barke a farkon watan Satumbar shekarar da ta shige.

Jami'an Nijeriya suka ce zaman tankiya ta karu tsakanin Musulmi da Kiristocin yankin na Jos a saboda dalilai da dama, ciki har da nada wani Musulmin da aka yi a shekarar da ta shige domin ya shugabanci wata hukumar gwamnati.

XS
SM
MD
LG