Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Tsohon Shugaban Sojan Ivory Coast, Janar Robert Guei, A Yunkurin Juyin Mulki A Kasar - 2002-09-19


An kashe ministan harkokin cikin gidan kasar Ivory Coast, Emile Boga Doudou, da tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar, Janar Robert Guei, a wani yunkurin juyin mulkin da aka yi a Abidjan, birni mafi girma a kasar.

A yanzu an ce kura ta lafa a birnin, bayan da aka shafe sa'o'i da yawa ana jin kararrakin bindigogi da na fashe-fashe, lamarin da ya faro tun daga misalin karfe 3 na dare.

An kashe wadannan mutane biyu a gwabzawar da aka yi a tsakanin sojoji masu yin bore da kuma masu biyayya ga gwamnati. Rahotanni suka ce wasu mutanen guda 8 sun mutu, cikinsu har da wani kanar na soja.

Wakiliyar Muryar Amurka a birnin Abidjan, Kate Davenport, ta ce kararrakin harbe-harbe da fashe-fashe daga wasu sansanonin soja biyu sun tayar da mazauna birnin Abidjan daga barci a cikin talatainin dare.

Firayim minista Afi Nguessan ya ce sojoji masu biyayya ga gwamnati suna aikin maido da kwanciyar hankali, a bayan da wasu sojoji suka nuna bijirewa domin rashin yarda da shirye-shiryen sallamar da za a yi ma wasu daruruwan sojojin.

Shaidu sun bada rahoton ganin wasu mutane cikin fararen kaya suna bai wa hammata iska a kan tituna.

Rahotanni sun ce a bayan birnin Abidjan, an kuma samu barkewar fada a wasu sansanonin sojan guda biyu, daya a garin Bouake dake tsakiyar kasar, dayan kuma a birnin Korhogo na arewaci.

Shugaba Laurent Gbagbo dai yana ziyarar aiki a kasar Italiya.

Da alamun sojojin masu bore sun fusata ne cewar za a kori abokan aikinsu 750 karfi da yaji. An dauki wadannan sojoji aiki a zamanin tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja Robert Guei.

Janar guei ya kwace mulki a wani juyin mulkin da ba a zubar da jini ba lokacin gudanar da shi a watan Disambar 1999.

Kasar Ivory Coast, wadda ake dauka a zaman wadda ta fi zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka ta yamma, ta fada cikin rikicin siyasa a bayan zaben watan Oktobar 2000, lokacin da aka hana shugaban hamayya, Alassane Ouattara tsayawa takara a zabe.

XS
SM
MD
LG