Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Birnin Bouake A Ivory Coast Suna Zaman Dar-Dar - 2002-09-23


Mazauna birnin Bouake dake hannun 'yan tawaye a yankin arewacin Ivory Coast, suna zaman jiran farmakin da ake kyautata zaton sojojin gwamnati zasu kai domin sake kwato wannan birni.

Rahotannin kafofin labarai sun ce an yi ta jin kararrakin harbe-harbe jefi-jefi yau litinin da safe a Bouake. Har yanzu dai babu wani labari na gocewar fada gadan-gadan.

Hukumomin Ivory Coast sun ce sojoji masu yin biyayya ga gwamnati sun kewaye birnin, kuma a shirye suke su kai farmaki idan har 'yan tawayen ba su mika wuya ba. Su ma shugabannin 'yan tawayen, sun ce a shirye suke su gwabza fada idan har bukatar hakan ta taso.

A ranar lahadi, dukkan sassan biyu sun nuna aniyar fara yin shawarwarin neman zaman lafiya.

A halin da ake ciki, sojojin Faransa sun isa Yamoussoukro, babban birnin kasar, domin kwashe Faransawa da 'yan kasashen waje idan har fada ya barke a Bouake dake kusa da nan.

Sojoji 750 sun yi bore ranar alhamis, inda suka kai hare-hare kan sojoji masu biyayya ga gwamnati a Bouake, da birnin Korhogo a arewacin kasar, da kuma cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar, Abidjan.

Sojojin masu yin tawaye suka ce suna bayyana rashin jin dadinsu ne da shirin gwamnati na sallamarsu daga aikin soja.

Gidan telebijin na kasar ya ce an kashe mutane akalla 270 a wannan fada, cikinsu har da tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja, Janar Robert Guei, da iyalansa. Gwamnati ta zargi Janar Guei da laifin kitsa wannan tawayen. Su kuma 'yan tawayen sun kashe ministan harkokin cikin gida, Emile Boga Doudou.

XS
SM
MD
LG