Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yayi Marhabin Da Rahoton Da Britaniya Ta Bayar Kan Shirin Iraqi Na Kera Makamai - 2002-09-24


Shugaba bush yayi marhabin da wani kundin da kasar Britaniya ta gabatar kan shirin Iraqi na kera makamai, yana mai bayyana kundin a zaman shaidar cewa shugaba Saddam Hussein mai barazana ne ga zaman lafiya.

Mr. Bush ya yabawa firayim minista Tony Blair na Britaniya saboda abinda ya kira shugabanci kwakkwara da ya nuna, a bayan da Mr. Blair ya gabatar da wannan kundin shaida mai shafi 55 a yau.

Mr. Blair ya shaidawa zama na musamman na majalisar dokokin Britaniya cewar shirin Iraqi na kera makamai masu guba yana nan daram, yana kuma kara bunkasa.

Wannan rahoto ya bayyana cewa Iraqi tana iya girka makaman da aka haramta mata mallaka cikin kasa da sa'a daya.

Har ila yau rahoton yayi kagen cewa shugaba saddam Hussein na Iraqi yana kokarin sayen "karfen Uranium mai yawa" daga nahiyar Afirka, karfen dake zaman sinadari mafi muhimmanci wajen kera makaman nukiliya.

A can wani gefen kuwa, Iraqi ta ce ta yanke shawarar kyale sufetocin makamai na MDD da su koma cikin kasar ba tare da tsangwama ba, a wani yunkurin da ta ce zai karyata rahoton da Britaniya ta buga cikin kundin dake zargin wai ita Iraqin tana ci gaba da kokarin kera makaman kare-dangi.

A lokacin da yake magana a birnin Bagadaza, mashawarcin gwamnati, Amr Saadi yayi watsi da rahoton na Britaniya, yana mai bayyana shi a zaman garwayen karya da gaskiya, da karyar tsagwaronta, da kuma zargi na rashin hangen nesa.

Janar Saadi ya ce kowa zai gane karyar wannan rahoto da firayim minista Tony Blair ya gabatar da zarar sufetocin makaman sun koma kasar Iraqi.

XS
SM
MD
LG