Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Zasu Isa Ivory Coast A Yau - 2002-09-24


Sojojin Amurka zasu isa Afirka ta Yamma a yau talata, domin kare Amurkawan da aka rutsa da su a fadan da ake gwabzawa a kasar Ivory Coast.

Tun farko jami'an sojan Amurka, sun ce zaratan sojoji 200 sun doshi Ivory Coast daga nahiyar Turai, amma a yanzu sun ce watakila sojojin zasu fara yada zango a kasar Ghana.

Wata sanarwar da aka bayar daga baya tayi gyaran cewa rundunar sojojin Amurka a turai zata tura sojojin kusa-kusa ta yadda zasu iya tabbatar da kare Amurkawa.

Tura wadannan sojojin da aka yi ya zo a daidai lokacin da fada ya kara yin muni a tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawaye a birnin Bouake na arewacin kasar, inda aka rutsa da wasu yara Amurkawa su 100 tare da wasu mutanen a cikin wata makarantar mishan.

Sojoji masu tawaye suna rike da Bouake da wasu yankuna da dama na arewacin kasar tun lokacin da suka tayar da kayar baya a ranar alhamisar da ta shige, ciki har da kai farmaki Abidjan, birni mafi girma a kasar. Birnin na Abidjan dai yana hannun gwamnati.

Su ma sojojin Faransa, wadda tayi wa Ivory Coast mulkin mallaka, suna kasar domin kare 'yan kasashen waje, cikinsu har da dubban 'yan kasar Faransa.

XS
SM
MD
LG