Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun 'Yan Tawayen Kasar Chadi Ya Mutu - 2002-09-24


Madugun 'yan tawayen kasar Chadi, Youssouf Togoimi, ya mutu yau talata a wani asibitin kasar Libya, a sanadin raunukan da ya samu lokacin wani hadarin taka nakiya cikin watan da ya shige.

Mr. Togoimi, tsohon ministan tsaro, ya rungumi makami ya fara yakar gwamnatin shugaba Idris deby tun shekarar 1999 a arewacin kasar, a lokacin da ya kirkiro da "Kungiyar Tabbatar Da Dimokuradiyya Da Adalaci A Chadi" ko MDJT a takaice.

A cikin watan Janairu, gwamnati da kungiyar ta MDJT sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiyar da Libya ta kulla tsakaninsu. Amma kuma Mr. Togoimi ya ki yarda da yarjejeniyar, kuma an ci gaba da gwabza fada jefi-jefi.

XS
SM
MD
LG