Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan majalisar Dokokin Ukraine Sun Fara Yajin Cin Abinci A Cikin Fadar Shugaban Kasar - 2002-09-24


Shugaba Leonid Kuchma na Ukraine ya ki yarda ya gana da 'yan adawa a majalisar dokokin kasar a birnin Qib, yayin da dubban 'yan zanga-zanga suka yi maci suna neman da yayi murabus.

Shugabannin adawa sun ce 'yan majalisar dokoki su akalla 50 sun fara yajin cin abinci a cikin ofishin shugaban kasar, kuma zasu ci gaba da zama a can har sai shugaba Kuchma ya gansu.

Tun da fari, 'yan majalisar dokokin masu adawa da Mr. Kuchma sun yi kokarin gabatar da kudurin tsige shugaban, amma sun kasa samun kuri'un da suke bukata domin gabatar da wannan kuduri ta yadda za a yi muhawara a kai.

'Yan adawar suna zargin shugaban na Ukraine da laifin zarmiya da kuma sa hannu wajen kashe wani dan jarida mai sukar lamirin gwamnati.

Shugaba Leonid Kuchma ya musanta dukkan zargin.

XS
SM
MD
LG