Sojojin Fasransa sun fara gadin wata makarantar mishan a kasar Ivory Coast, inda fada a tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawaye ya rutsa da 'yan kasashen waje.
A yau laraba sojojin na Faransa suka kutsa ta cikin bakin daga a birnin Bouake, domin kare wannan makaranta, inda yara Amurkawa su kimanin 100 tare da wasu 'yan kasashen waje suka nemi mafaka tun ranar alhamis, lokacin da wasu sojoji suka fara yin bore.
Turawan mishan a wurin sun ce dalibai da malaman ba su son a kwashe su a saboda zuwan sojojin Faransa ya kwantar musu da hankula.
A yau laraba kuma, an ci gaba da gwabza fada jefi-jefi a Bouake a yayin da sojojin gwamnati ke kokarin tumbuke 'yan tawaye daga cikin birnin.
Sojojin Amurka, sun isa Ghana makwabciyar Ivory Coast jiya talata da maraice, domin taimakawa wajen kwashe 'yan kasashen waje idan bukatar hakan ta taso.
A halin da ake ciki, daruruwan magoya bayan gwamnati sun yi gangami a kofar ofishin jakadancin Faransa yau laraba a birnin Abidjan, domin nuna fusatarsu da mafakar da Faransa ta bai wa madugun 'yan adawa, Alassane Ouattara. Malam Ouattara ya ce 'yan sanda sun yi kokarin kashe shi a lokacin da wannan fitina ta barke.