Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Ce Babu Ruwanta Da Harin Da Aka Kai Kan Wurin Ibadar Hindu A Indiya - 2002-09-25


Pakistan ta yi watsi da zargin da Indiya ta yi cewar akwai hannun ita Pakistan a mummunan harin da aka kai jiya talata a kan wani wurin ibadar Hindu a yammacin kasar Indiya.

Wani kakakin Pakistan yayi tur da harin, yana kuma bayyana zargin da aka yi wa kasarsa da cewa zancen banza ne. Ya ce wadanda suka kai harin suna kokari ne su kara zafafa zaman tankiya a wannan yanki.

Hukumomin Indiya sun girka sojoji kimanin dubu uku a Jihar Gujarat domin rigakafin barkewar rikicin addini a bayan wannan harin da aka kai kan wurin ibadar.

Wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, sun kashe masu ibada su 30 kafin sojojin kundumbala su abka cikin wannan gini su kashe 'yan bindiga biyu yau laraba da asubahi.

Mukaddashin firayim ministan Indiya, L.K. Advani, ya ziyarci wurin ibadar a yau laraba, inda yake bayyana cewar watakila Pakistan ce ta shirya kai harin.

XS
SM
MD
LG