Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasashen Waje Suna Gudu Daga Wani Birni A Kasar Ivory Coast - 2002-09-27


'Yan kasashen waje su akalla dubu daya sun tsere daga birnin Bouake na kasar Ivory Coast, yayin da sojojin gwamnati ke barazanar kai farmaki gadan-gadan kan wannan birni.

Rahotanni daga birnin na Bouake dake tsakiyar Ivory Coast sun ce jiya alhamis da maraice zuwa cikin dare aka kwashe 'yan kasashen Ingila da Faransa da Amurka. Gudun da bakin ke yi ya biyo bayan gargadin da ministan tsaron Ivory Coast, Moise Lida Kouassi, yayi cewar nan bada jimawa ba sojojin gwamnati zasu kai farmaki domin kwato birnin.

Sojojin Faransa suna ci gaba da raka 'yan kasashen waje dake gudu daga Bouake, sun kuma ce yau Jumma'a da maraice zasu kammala wannan aiki.

A ranar laraba, an kwashe Amurkawa kusan 200 yara 'yan makaranta da malamansu daga Bouake, kuma a jiya alhamis aka kwashe su ta jirgin sama zuwa Ghana.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta shawarci Amurkawa da kada su yi tafiya zuwa kasar Ivory coast, ta kuma yi kira ga wadanda ke can da su bar kasar.

An kashe mutane kusan 400 a tashin hankalin da ya barke tun lokacin da wasu sojoji suka fara yin bore a makon da ya shige. Mutane akalla 270 sun mutu a Abidjan ranar alhamisar makon jiya, amma nan da nan sojojin gwamnati suka magance 'yan tawaye a can.

XS
SM
MD
LG