Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Masu Yin Tawaye Sun Sake Kwace Wani Garin A Kasar Ivory Coast - 2002-09-27


Sojoji masu yin tawaye a kasar Ivory coast sun kwace garin Odienne a arewacin kasar, yayin da mazauna wani garin dabam dake hannun 'yan tawaye suke shirye-shiryen fuskantar farmaki daga sojojin gwamnati.

Mazauna birnin Bouake dake firgice, suna kokarin gudu, amma kuma 'yan tawayen da suka kafa shingaye kan hanyoyin mota suna mayar da su baya zuwa cikin wannan birni wanda shine na biyu wajen girma a kasar.

Tun fari, a yau Jumma'a sojojin Faransa suka kammala aikin kwashe 'yan kasashen waje su dubu daya daga birnin.

Mazauna garin Odienne dake bakin iyaka da kasar Guinea, da kuma jami'ai sun ce 'yan tawaye sun shiga garin a cikin daren jiya alhamis, suna harbin iska. Suka ce sojojin gwamnati dake garin sun gudu, yayin da 'yan tawayen suka mamaye gine-ginen gwamnati ciki har da ofisoshin 'yan sanda.

Odienne shine gari na baya-bayan nan da ya fada hannun 'yan tawaye tun lokacin da aka fara tunzuri a makon da ya shige.

Mutane kimanin 400 sun mutu a wannan fitina ta kasar Ivory Coast.

Ranar lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wani taron kolin yankin Afirka ta Yamma a kasar Ghana domin tattauna wannan fitina ta Ivory Coast.

XS
SM
MD
LG