Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Swaziland Ta Soke Shirin Sayen Jirgin Saman Dala Miliyan 50 Ma Sarkin Kasar... - 2002-09-30


Hukumomin kasar Swaziland sun bada sanarwar soke shirin sayen jirgin saman dala miliyan 50 ma sarkin kasar, matakin da a bisa dukkan alamu zai kawo karshen caa din da aka yi wajen sukar lamirin gwamnati a wannan kasa mai fama da talauci.

Firayim minista Sibusiso ya bayar da takardar sanarwa a yau litinin, inda yake fadin cewa a maimakon sayen jirgin, gwamnati zata nazarci yiwuwar yin hayar wani jirgi domin tafiye-tafiyen da sarkin zai yi.

Mutane da yawa a kasar dake yankin kudancin Afirka, da kuma jami'an Kungiyar Tarayyar Turai, sun bayyana fusata dashawarar gwamnati ta kashe wannan kudi mai dimbin yawa a yayin da kasar take cikin mummunar matsala. Rubu'i, ko kuma kashi daya bia hudu, na al'ummar wannan kasa su miliyan daya suna fuskantar bala'in yunwa a cikin wannan shekara.

XS
SM
MD
LG