Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lili Ta Zamo Mahaukaciyar Guguwa Mai Tafe Da Ruwan Sama - 2002-09-30


Hadarin ruwan sama mai tsananin karfi da ake kira "lili" ya rikide ya koma mahaukaciyar guguwa mai dauke da ruwan sama. A yanzu, Lili ta doshi tsibiran Cayman Islands da Cuba tattare da iska mai tsananin karfi da kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya.

An ce a yanzu Lili tana tafe da iska mai juyawar kilomita 120 cikin sa'a daya. Tsakiyar wannan mahaukaciyar guguwa, watau inda ta fi tsanani, yana daidai kan tsibiran Little Cayman da Cayman Brac.

Har yanzu ba a samu rahoton barna a wannan tsibirin da Britaniya take mulkinsa ba, wanda kuma cibiya ce babba ta hada-hadar kudi a duniya.

A jiya lahadi, Lili ta ratsa ta kan tsibirin Jamaica, inda mutane akalla hudu suka mutu lokacin da ruwan ambaliya yayi awon gaba da su.

XS
SM
MD
LG