Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar ECOWAS Ta Doshi Ivory Coast - 2002-09-30


Jami'an yankin Afirka ta Yamma zasu yi tattaki zuwa Ivory Coast domin shiga tsakanin gwamnati da sojojin kasar dake yi mata tawaye.

A bayan sun gana yau litinin da shugaba Laurent Gbagbo, ministocin harkokin waje da na tsaro dake cikin tawagar suna fatan shirya ganawa da sojoji masu tawaye dake rike da biranen Bouake da wasu garuruwa na arewacin Ivory Coast.

An kafa wannan tawaga jiya lahadi, a lokacin wani taron gaggawar da aka yi na Kungiyar Kasuwar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, a Accra, babban birnin Ghana.

Shugabannin ECOWAS sun yarda cewa kasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da Guinea-Bissau da kuma Togo sune zasu jagoranci wannan kokari na sasantawa.

Shugabanni a wurin taron na ECOWAS sun bayyana goyon baya ga shugaba Gbagbo, sun kuma ce zasu tura runduna ta kasa da kasa ta sojoji dubu hudu idan har kokarin sasanta tsakanin sassan ya ci tura.

Wannan kokarin sasantawa ya biyo bayan kwashe daruruwan 'yan kasashen wajen da sojojin Amurka da na Faransa suka yi jiya lahadi daga garin Korhogo na arewacin kasar, wanda ke hannun 'yan tawaye.

A hedkwatar MDD, jakadan kasar Ivory Coast, Djessan Philippe Djangone-Bi, ya ce kasarsa tana son yakar 'yan tawayen da kanta. Ya ce rundunar sojan kasar tana sabunta makamanta, tana kuma bukatar karin makamai daga wasu kasashe domin murkushe wannan tawaye. Ya ce tuni har sojoujin Faransa sun taimaka da kayan fada.

Har ila yau, Mr. Djangone-Bi yayi zargin cewa 'yan tawayen suna samun agajin makamai daga wasu kasashe, amma bai fadi ko su wanene ba. Sai dai kuma ya ce 'yan tawayen sun samo asali ne daga Burkina Fasso da Saliyo da kuma Liberiya. Babu wata kafar da ta gaskata wannan ikirari nasa.

A yau litinin, gwamnatin Ivory Coast ta ce ta kara tsawon wa'adin aiki da dokar hana yawon daren da ta kafa a fadin kasar tun lokacin da aka fara wannan tawaye.

XS
SM
MD
LG