Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tony Blair Ya Ce Akwai Bukatar Zartas Da Kuduri Mai Tsauri A Kan Iraqi - 2002-10-03


Firayim minista Tony Blair na Britaniya ya ce yana da matukar muhimmanci ga Kwamitin Sulhun MDD da ya kafa sabon kuduri mai tsaurin gaske kafin sufetocin makamai su koma kasar Iraqi.

Mr. Blair ya shaidawa gidan rediyon Britaniya cewa sabon kudurin zai zamo hannunka mai sanda ga Iraqi kan ta kaucewa tayar da fitina. Ya ce kudurorin binciken makamai na baya ba su da tsaurin da zasu iya tabbatar da cewa an gudanar da aikin yadda ya kamata.

Mr. Blair ya ce shugaba Saddam Hussein na Iraqi yana iya mallakar rundunar sojoji da makamai na yau da kullum, amma kuma ban da makaman nukiliya ko masu guba ko kuma na yada kwayoyin cuta.

Amma a can wani gefen kuma, Rasha da Faransa da kuma China sun sake nanata cewa ba su da aniyar amincewa da a bada iznin yin amfani da karfin soja har sai an bai wa sufetocin makamai lokacin gwada cewa ko da gaske ne Iraqi tana da aniyar bada hadin kai wajen gudanar da binciken.

Mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha, Alexander Saltanov, ya ce kasarsa tana yin adawa da duk wani lafazin da ya ambaci yin amfani da karfi kai tsaye a cikin duk wani sabon kudurin MDD.

Shi ma shugaba Jacques Chirac na Faransa, jiya laraba ya sake jaddada adawarsa da duk wani kudurin MDD da zai ce ana iya yin amfani da karfin soja a kan Iraqi kai tsaye ba tare da an sake neman iznin majalisar ba.

Ita kuma ma'aikatar harkokin wajen China ta bada sanarwar a yau alhamis, inda take cewa babban aikin dake gaban Kwamitin Sulhun MDD a wannan lokacin shine na tabbatar da cewa sufetocin makamai sun koma Iraqi, tare da kyale su su gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba.

XS
SM
MD
LG