Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Sake Jaddada Adawarta Da Zartas Da Wani Sabon Kudurin MDD A Kan Iraqi - 2002-10-04


Rasha ta sake jaddada adawarta da kafa duk wani sabon kudurin Kwamitin Sulhun MDD a kan Iraqi, ta kuma yi kiran da a gaggauta mayar da sufetocin makamai zuwa Iraqi.

Mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha, Yuri Fedotov, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Itar-Tass cewa kudurorin da ake da su a yanzu kan matsalar ta Iraqi sun wadatar.

Wannan furuci nasa ya zo kwana guda a bayan da ministan harkokin wajen Rasha, Igor Ivanov, da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell suka tattauna batun na Iraqi ta wayar tarho. Mr. Ivanov ya jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa ka'in da na'in game da batun na Iraqi a tsakanin wakilan Kwamitin Sulhu.

Rasha tana da huldar tattalin arziki mai karfi da Iraqi, kuma tana yin adawa da daukar duk wani matakin soja kan shugaba Saddam Hussein.

A halin da ake ciki, jami'an Iraqi sun ce za a ci gaba da aiwatar da shirin tattalin arziki na shekaru biyar da kasar Rasha.

Shugaban wata tawagar Iraqi dake ziyartar Rasha cikin wannan mako, Abdel-Razaq al-Hashimi, ya musanta cewa wannan shiri na dala miliyan dubu 40 kokari ne na sayen goyon bayan Rasha.

XS
SM
MD
LG