An dakatar da bukin sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar da zata kawo karshen boren makonni biyu a kasar Ivory Coast.
Jami'an shiga tsakani daga kasashen Afirka ta Yamma sun ce jami'an gwamnatin Ivory Coast sun bayyana adawarsu da kalamun da suka yi magana a kan rundunar kiyaye zaman lafiya ta yanki.
Su kuma 'yan tawaye sun bayyana dari-dari da sassan shirin da suka bukace su da su kwance damarar yaki, su kuma mika yankunan dake hannunsu a arewacin kasar.
Jami'ai masu shiga tsakani suka ce har yanzu suna fatar za a rattaba hannu kan yarjejeniyar nan gaba a yau a Yamoussoukro, babban birnin kasar, inda sojojin Faransa suke gudanar da ayyukan tsaro.
Jiya alhamis aka bada sanarwar bukin rattaba hannu kan yarjejeniyar a bayan da masu shiga tsakani suka gana da 'yan tawayen a birnin Bouake.