Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Gwamnatin Ivory Coast Sun Shiga Cikin Tungar 'Yan Tawaye - 2002-10-07


Sojojin gwamnatin Ivory Coast sun kutsa cikin tungar 'yan tawaye a Bouake, a bayan da aka gwabza kazamin fada.

Mazauna wannan birni, wanda shine na biyu wajen girma a kasar, sun ce sun ga motocin soja na gwamnati guda uku suna zirga-zirga yau litinin cikin wasu unguwannin fararen hula. Wannan shine karon farko cikin makonni uku da wata unguwa a wannan birni ta fita daga hannun 'yan tawaye.

Jiya lahadi gwamnati ta kaddamar da gagarumin farmaki kan cibiyoyin 'yan tawaye a wannan birni dake tsakiyar kasar, a bayan da shugaba Laurent Gbagbo ya ki sanya hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wutar da masu shiga tsakani na Afirka ta Yamma suka kulla.

Sojojin 'yan tawayen, wadanda akasarinsu Musulmi ne daga arewavcin kasar, sun kame Bouake da wasu yankunan arewacin kasar suka rike tun ranar 19 ga watan Satumba, lokacin da suka fara yin bore. Mutane kimanin 400 suka mutu a wannan tashin hankali, cikinsu har da ministan harkokin cikin gida da wani tsohon shugaban sojan kasar.

XS
SM
MD
LG