Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Tana Binciken Musabbabin Bindigar Da Jirgin Ruwan Daukar Manta Yayi A Kusa Da Yemen - 2002-10-07


Faransa ta aike da masu bincikenta zuwa Yemen, domin bin diddigin bindiga da kuma wutar da ta wakana cikin wani jirgin ruwan jigilar mai na Faransa, yayin da ake samun rahotanni kishiyoyin juna kan ko wannan lamari hadari ne, ko kuma da gangan aka haddasa shi.

Kamfanin dillancin labaran Yemen, SABA, ya bada rahoton cewa wasu kwararru daga Faransa sun isa can yau litinin da maraice domin bin sawun wannan lamari.

A daidai wannan lokacin kuma, jami'an shari'a na Faransa sun ce sashen kula da ayyukan ta'addanci na ofishin lauayn gwamnati mai gabatar da kararraki, ya fara gudanar da binciken share fage game da fashewar da ta abku cikin tankar man.

Wannan jirgin ruwan tanka da ya lalace yana galantoyi yanzu haka cikin mashigin ruwan Aden, yayin da kamfanin dillancin labaran Faransa ya bada rahoton cewa an fara ganin man dake tsiyaye a kan ruwa a gabar kasar Yemen.

An ceto ma'aikatan jirgin 24, yayin da cikon na 25 ya bata ba a san inda yake ba har yanzu.

XS
SM
MD
LG