An kashe masu hakar gwal su biyu, aka raunata wasu guda 14 a lokacin da masu gadi suka yi harbi a kan ma'aikatan hakar ma'adinai masu yajin aiki a Afirka ta Kudu.
Kamfanin dillancin labaran Afirka ta Kudu, ya ambaci wani jami'in kungiyar kwadago yana fadin cewa an harbe ma'aikatan guda biyu a lokacin da masu gadi suke kokarin korar ma'aikata daga kusa da bakin wani ramin hakar ma'adinai.
Ma'aikatan hakar ma'adinan suna yajin aiki ne a saboda rikici kan albashi a ramukan hakar ma'adinan East Rand dake garin Boksburg a kusa da birnin Johannesburg.