Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Bindigar Washington Ya Sake Yin Kisa - 2002-10-15


'Yan sanda a Jihar Virginia dake makwabtaka da nan birnin Washington sun tabbatar da cewa kashe wata mace da aka yi a daren jiya litinin, aikin dan kwanton-baunar nan ne dake karkashe mutane haka siddan a nan yankin birnin na Washington.

Baturen 'yan sanda na yankin karamar hukumar Fairfax a Jihar Virginia, Tom Manger, ya ce sakamakon nazarin harsashin da aka yi, ya nuna cewa bindigar da aka kashe Linda Franklin mai shekaru 47 da haihuwa, ita ce aka yi ta amfani da ita wajen harbe-harben da aka faro tun ranar 2 ga watan Oktoba.

An harbe Mrs. Franklin aka kashe ta a wurin ajiye motoci na wani makeken kanti a garin Falls Church a lokacin da ta bude bayan motar take zuba abubuwan da suka sayo daga kantin tare da mijinta.

'Yan sanda suna neman wata fara, ko fara-farar motar daukar kaya da aka gani kusa da inda aka harbe matar. Mr. Manger ya ce 'yan sanda sun samu karin bayani a game da harbin na daren jiya, kuma yana da kwarin guiwar cewa bayanin yana iya kaiwa ga gano wannan shu'umi.

Amma bai bayyana ko menene ba. Haka kuma ya ki ya ce uffan game da wasu rahotannin da aka bayar cewa motar tana dauke da lambar jihar Maryland.

Jami'an tsaro na tarayya da jihohi da kananan hukumomi, wadanda suka hada karfi wuri guda suna binciken harbe-harben dan kwanton-baunar a nan yankin Washington, sun ce suna binciken daruruwan rahotannin da jama'a suka ba su.

A yanzu dai tukuicin da za a bada duk wanda ya taimaka wajen kamo wannan shu'umi ya kai dala dubu 500, ko kuma naira miliyan 65.

XS
SM
MD
LG