Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Yarda Zata Taimaka Wajen Tabbatar Da Yin Aiki Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Ivory Coast - 2002-10-18


A yau jumma'a aka fara yin aiki da shirin tsagaita wuta a kasar Ivory Coast, a bayan da dakarun 'yan tawaye suka rattaba hannu a kai.

Tun fari a yau jumma'a, shugaba Laurent Gbagbo ya amince da yarjejeniyar tsagaita wutar cikin jawabin da yayi ga al'ummar kasar ta telebijin.

Da alamun ana yin aiki da shirin tsagaita wutar, tun da ba a samu wani rahoton fada ba tun daga lokacin da shirin ya fara da karfe 12n daren da ya shige. Masu shiga tsakani sun ce a yanzu hankali zai koma kan karin tattaunawa a tsakanin sassan biyu, tattaunawar da jami'an gwamnati suka ce ana iya farawa ranar talata.

'Yan tawayen sun yarda da tsagaita wuta jiya alhamis, a bayan tattaunawar mintoci 90 da masu shiga tsakani a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Senegal, Cheikh Tidiane Gadio, a birnin Bouake dake hannun 'yan tawayen.

A karkashin yarjejeniyar, dukkan sassan biyu zasu daina fada, amma kuma ba a bukaci kowane bangare da ya ajiye makamansa ba. Amma kuma an tanadi cewa dukkan sassan zasu daina kai farmaki kan juna, kowa ya tsaya a inda yake a yanzu.

A yau Jumma'a, Faransa ta yarda da rokon da shugaba Laurent Gbagbo yaui mata na a yi amfani da sojojin Faransa dake Ivory Coast a yanzu wajen kula da shirin tsagaita wutar. Zasu bada wannan gudumawa har zuwa makon gobe, a lokacin da kungiyar ECOWAS zata kaddamar da nata aikin na sanya idanu kan yadda ake aiki da shirin tsagaita wutar.

XS
SM
MD
LG