Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Rahoto Ya Ce Pakistan Ta Taimakawa Koriya Ta Arewa Wajen Kera Makamin Nukiliya - 2002-10-18


Jaridar New York Times ta ce jami'an leken asirin Amurka sun yi imanin cewa Pakistan ce ta samar da kayayyaki masu muhimmancin da ake bukata ga shirin asirin da Koriya ta Arewa ta bayyana kwanakin baya na kera makamin nukiliya.

Jaridar, wadda ta ambaci sabbi da tsoffin manyan jami'an gwamnatin Amurka, sun ce kayayyakin watakila sun hada da injuna sarrafa makamashi na iskar gas wadanda ake yin amfani da su wajen tace karfen Uranium ta yadda za a iya hada makami da shi.

Jami'ai suka ce da alamun wadannan injuna an yi musanyarsu ne tsakanin Pakistan da Koriya ta Arewa a wani cinikin ba ni gishiri in ba ka manda da suka yi a karshen shekarun 1990.

Domin ramawa kura aniyarta a karkashin wannan shirin, an ce Koriya ta Arewa ta samarwa da Pakistan makamai masu linzamin da zata iya amfani da su wajen takalar makaman nukiliyar da kasar Indiya take da su.

Pakistan ta bayyana wannan rahoton da cewa ba ya da tushe. Amma Indiya ta bayyana damuwa a game da rahotannin.

XS
SM
MD
LG