Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Eritrea Ta Zargi Amurka Da Kokarin Yi Mata Makarkashiya - 2002-10-21


Eritrea ta zargi Amurka da kokarin hambarar da gwamnatinta lokacin yakin shekaru biyu da suka gwabza da Ethiopia.

Ma'aikatar harkokin wajen Eritrea ta bayar da sanarwa inda take fadin cewa tsohuwar gwamnatin shugaba Bill Clinton tayi amfani da hukumar leken asirin Amurka ta CIA domin hayar manyan jami'an Eritrea a lokacin yakin da kasar tayi da Ethiopia daga 1998 zuwa 2000. Ta ce gwamnatin shugaba Clinton tayi kokarin yin amfani da jami'an domin kafa sabuwar gwamnati a Asmara.

Wannan zargi ya biyo bayan bukatar da Amurka ta gabatar a makon jiya, cewar a sako wasu 'yan kasar ta Eritrea su biyu da suka yi aiki ma ofishin jakadancin Amurka. Yau fiye da shekara guda ke nan ana rike da mutanen ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi ba.

har ila yau ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana damuwa kan abinda ta bayyana a zaman keta hakkin bil Adama da gwamnatin Eritrea take aikatawa.

ma'aikatar harkokin wajen Eritrea ta musanta wannan zargin, ta kuma yi kira ga Amurka da ta daina yin katsalanda a harkokin cikin gida na Eritrea ba tare da wata hujja ba.

XS
SM
MD
LG