Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Ce Ba Zata Mikawa Kamaru Yankin Bakassi Ba... - 2002-10-23


Nijeriya ta ce ba zata mika wa kasar kamaru yankin nan na Bakassi mai arzikin man fetur ba, wanda kotun duniya ta ce mallakar ita Kamaru ne.

Ministan sufurin Nijeriya, Ojo Maduekwe, ya karanta sanarwa a bayan taron majalisar zartaswa ta kasa yau laraba a Abuja, inda yake cewa kotun duniyar, "...ta dauki wani matsayin shari'a wanda ya sabawa dukkan dokokin da aka sani da kuma yarjejeniyoyi." Ministan ya zargi alkalan kotun da dama da laifin nuna goyon baya irin na 'yan mulkin mallaka.

Dukkan alkalan kotun 'yan kasashen Turai ne, kuma suna karkashin jagorancin wani alkali daga Faransa, kasar da ta yi wa Kamaru mulkin mallaka.

A hukumcin da ta yanke ranar 10 ga watan Oktoba, kotun ta duniya ta amince da hujjar Kamaru cewa an maida wannan tsibiri ya zamo bangaren kasarta a karkashin wata yarjejeniyar da turawa 'yan mulkin mallaka na jamus da Ingila suka kulla a shekarar 1913.

Abubuwan da kasashen biyu ke hankoro a wannan yanki na Bakassi sune danyen man fetur mai yawa da aka ce yana kwance a karkashin yankin, da kuma kifi mai yawa a ruwayen wannan yanki.

A can baya, Nijeriya da Kamaru duk sun yarda cewar zasu mutunta hukumcin kotun. Kasashen sun sha gwabza yaki domin neman mallakin yankin na Bakassi wanda ba a zayyana bakin iyakarsa sosai ba a lokacin mulkin mallaka.

Nijeriya da Kamaru sun girka sojojinsu a fadamun yankin dake mashigin ruwan Guinea. Hukumcin kotun ta duniya dai ba a iya daukaka shi.

Mazauna yankin Bakassi suna daukar kansu a zaman 'yan Nijeriya, kuma sun sha yin barazanar cewar zasu balle su kafa kasarsu 'yantacciya idan har gwamnatin Nijeriya ta yarda ta mika yankin ga Kamaru.

A cikin sanarwar da ya karanta din, ministan sufurin Nijeriya ya ce "har abada Nijeriya ba zata yi watsi da al'ummarta da kuma muradunsu ba. Ga Nijeriya, wannan ba batu ne na man fetur ko albarkatun kasa ko na ruwa dake yankin ba, batu ne na kulla da lafiyar 'yan kasarta da muradunsu a cikin kasarsu."

XS
SM
MD
LG