Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaure Da Kazamin Fada Kusa Da Fadar Shugaban Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya - 2002-10-28


Fada ya kara rincabewa yau litinin a tsakanin sojojin gwamnati da masu yin tawaye a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

An bada rahoton jin kararrakin manyan makamai a unguwannin arewacin birnin dake hannun sojoji masu yin tawaye. Wasu rahotannin sun ce ana gwabza fada a kusa da fadar shugaban kasar, wadda ba ta da nisa daga ginin majalisar dokoki a tsakiyar birnin na Bangui.

Ba a san inda shugaba Ange Felix Patasse na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya yake ba.

Magoya bayan tsohon hafsan sojojin kasar da aka tura gudun hijira, Francoise Bozize, sune suka kaddamar da wannan tawaye ranar Jumma'a da nufin hambarar da shugaban kasar. An bada rahoton kashe mutane akalla 20 ya zuwa yanzu. Wasu dubbai sun gudu tun lokacin da aka fara wannan fadan.

Gwamnati ta ce da yawa daga cikin masu tawayen sun fito ne daga kasar Chadi makwabciyarsu, inda Mr. Bozize ya gudu ya koma bayan da aka kore shi a shekarar da ta shige, saboda rawar da aka yi zargin ya taka a wani yunkurin hambarar da gwamnati a bara.

An yi imani da cewa 'yan tawaye suna rike da sulusin birnin na Bangui.

A jiya lahadi, sojojin gwamnati, tare da taimakon Libya, sun ce sun kewaye 'yan tawayen, sun kuma kiraye su da su mika wuya ko kuma a gama da su.

XS
SM
MD
LG