Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Tana Jimamin Wadanda Suka Mutu A Lokacin Da Sojoji Suka Yi Kokarin Ceto Wadanda Ake Garkuwa Da Su - 2002-10-28


Al'ummar Rasha suna jimamin mutane 117 da suka mutu a lokacin da 'yan tawayen Chechnya suka mamaye wani gidan wasa a Moscow. Im ban da biyu daga cikin wadannan mutane, duk saura sun mutu ne lokacin da suka shaki iskar gas da hukumomin Rasha suka dura cikin gidan wasan domin sumar da 'yan bindigar.

Koda yake hukumomin Rasha sun ki fadar sunan irin iskar gas da suka yi amfani da ita, sun musanta cewa iskar Sarin ce ko kuma wata iskar mai guba.

Jami'an Amurka suka ce sun yi imani wannan iskar Gas da sojojin Rasha suka hura cikin wannan gini, wadda ta samo asali ne daga kwaya dangin zakami.

Likitoci sun ce an sallami mutane fiye da 200 daga asibiti, amma har yanzu ana jinyar wasu mutanen su 405 a saboda iskar wannan gas da suka shaka.

Jami'an birnin Moscow, sun ce zasu bada diyyar kimanin dala dubu 3 da 100, ko Naira dubu 400 ga iyalan kowane mamaci, yayin da mutanen da suka tsira da rayukansu zasu samu rabin wannan adadi.

A can gefe, wani manzon shugaba Aslan Maskhadov na Chechnya ya ce jamhuriyar tana shirye ta tattauna neman zaman lafiya da Moscow ba tare da wani sharadi ba.

Mukaddashin firayim ministan Chechnya, Akhmed Zakayev, shine ya bayyana wannan a wurin taron duniya na Chechnya da aka bude yau litinin a Copenhagen, babban birnin kasar Denmark, duk da korafin da Rasha tayi kan wannan taron.

Rasha ta fito da kakkausar harshe tana sukar Denmark saboda kyalewar da tayi a gudanar da wannan taron kwanaki biyu, a bayan da 'yan bindigar Chechnya suka yi garkuwa da daruruwan mutane a gidan wasa a birnin Moscow.

Har ila yau, Rasha ta yi barazanar kauracewa wani taron koli da Tarayyar Turai, wanda aka shirya gudanarwa cikin wata mai zuwa a birnin na Copenhagen.

Daga baya, Denmark, wadda ke rike da kujerar shugabancin KTT har zuwa watan Disamba, ta ce za a dage wannan taro zuwa birnin Brussels.

XS
SM
MD
LG